
An shirya gudanar da jana’izar fitaccen jarumin nan wanda ya yi fafutukar yaki da wariyar launin fata a Afrika ta Kudu, kuma ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, a ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekara a babban cocin St George na Martyr a Cape Town.
Thabo Makgoba, Archbishop na Cape Town, ya sanar a ranar Litinin cewa, za a yi jana’izar marigayi Desmond Tutu, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.
“Da karfe 10 na safiyar ranar Asabar ta sabuwar shekarar 2022 ne za a yi jana’izar” inji shi.
Tun daga ranar Juma’a, gawar Desmond Tutu za a kaita babban cocin da ya yi hidima a tsawon shekaru masy yawa.
Yayin da ake ci gaba da samun karramawa daga sassa daban-daban na duniya, ‘yan garin na Cape town da ‘yan Afirka ta Kudu sun yi bikin karrama shugaban na masu adawa da wariyar launin fata.
Bayan rasuwar limamin cocin, shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kira da a gudanar da zaman makoki na kwanaki bakwai.
Archbishop Desmond Tutu ya rasu ne a ranar Lahadin nan da ta gabata.