Yunkurin samar da sabbin gundumomi a jihar Adamawa ya gamu da cikas
Shugabannin al’umma a Jimeta ta jihar Adamawa sun yi watsi da shawarar kirkirar sabbin gundumomi biyu a cikin garin Adamawa.
Babbar Tawaga karkashin jagorancin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa Muhammad Turaki, a ranar Larabar da ta gabata, sun bayyana matsayarsu ta hanyar mika sakonsu ga kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin jihar kan samar da karin gundumomi a Yola.
Turaki ya yi nuni da cewa, samar da sabbin gundumomi bai dace ba ta fuskar tattalin arziki, duba da yadda wasu gundumomin da ake da su ba za su iya biyan albashi na wasu watanni ba.
A nasa jawabin, Usman Wakili, tsohon mai baiwa tsohon Gwamna Murtala Nyako shawara kan harkokin siyasa, ya ce matakin bai samu goyon bayan mafi yawan al’ummar Jimeta ba.
A nasa martanin shugaban kwamitin kuma shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Hamman Tukur Yettisuri, ya tabbatar ma shugabannin al’umma cewa, majalisar za ta yi adalci kan abubuwan da suka gabatar tare da yin la’akari da dalilansu.
Sai dai ya nisanta gwamnatin jihar akan wannan yunkuri, inda ya bayyana cewa, “gwamnatin jihar ba ta da hannu a yunkurin samar da sabbin gundumomi.”