
Rahoton Daily Trust
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da wata babbar tawaga wadda ta hada da shugabannin hukumar leken asiri da tsaro ta kasa zuwa jihohin Sokoto da Katsina domin mayar da martani kan yawaitar ayyukan ‘yan fashi da makami.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaban kasar na sa ran samun rahoton halin da ake ciki cikin gaugawa da kuma shawarwari kan matakan da za su bi domin shawo kan lamarin da ya ke kara tsananta.
A safiyar ranar Juma’a ne dai matasa suka bazama kan tituna a wasu garuruwan arewacin kasar, inda suka yi kira ga shugaban kasar da ya magance matsalar rashin tsaro yadda ya kamata.
Wasu ‘yan bindiga sun kona wasu fasinjoji da ransu a ranar Litinin yayin da aka kashe wani kwamishina a Katsina ranar Laraba.