
Duk da yanayin alhini da ake fama da shi a Najeriya na kisa ta hanyar kona matafiya da ‘yan bindiga a Sabon birnin jihar Sokoto suka yi, wasu da ake kyautata zaton‘yan bindiga ne sun sake kai farmaki kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, inda suka kashe mutane uku
Majiyarmu ta ruwaito cewa,Harin dai ya faru ne sa’o’i kadan bayan Gwamna Aminu Tambuwal ya bar yankin.
Tambuwal ya ziyarci Sabon Birni ne domin kai ziyarar jaje ga iyalan matafiya da ‘yan bindiga suka kona kurmus a hanyar Sabon birni zuwa Isa ranar Litinin.
Gwamnan ya sanar da bayar da gudummawar Naira 250,000 ga iyalan da suka rasa danginsu.
Wakilin Daily trust, yaruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe takwas na daren jiya Alhamis, inda suka rika harbe-harbe.
“Sun zo ne a lokacin sallar magariba, suna harbi kai tsaye. Sun kashe mutanenmu uku tare da raunata wasu da dama wadanda a halin yanzu suke kwance a asibiti,” inji wani mazaunin garin.
Har zuwa hada wannan ruhoto ba a ji ta bakin kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar ba.