
Rundunar ‘yan sandan titin Shagamu, ta kama wani mutum mai suna Sikiru Kolawole dan shekara 41 da haihuwa,bisa zarginsa da mallakar sassan jikin dan adam a unguwar Ikoorodu da ke jihar Legas.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas, Mista Adekunle Ajisebutu,ya tabbatar da faruwar lamari. Ya ce an gano wanda ake zargin da sassan jikin dan adam sabbin diba da suka hada da hannaye, hanji, da kuma kokon kai daga makabartar Ojokoro da ke Ikorodu.
Ajisebutu ya ce; “Kwamishanan ‘yan sanda, Hakeem Odumosu, ya bayar da umarnin mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka (SCID) da ke Panti, Yaba, domin gudanar da zuzzurfan bincike, da kuma gurfanar da shi gaban kotu.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Ikorodu, Hon. Wasi’u Adesina, wanda ya jagoranci ‘yan majalisar karamar hukumarsa zuwa wurin da abin ya faru, ya yi alkawalin cewa majalisar karamar hukumar za ta samar da matakan da suka dace domin dakile wannan aika-aikar don kauce ma sake faruwar haka.
Ya kuma umurci sashen kula da muhalli da su share kowane bangare na makabartar ciki da waje, inda ya kara da cewa wanda ake zargin za a hukunta shi bisa doka domin ya zama darasi ga masu wannan hali.
A cewar shugaban majalisar; “A yayin da muke aiki don kula da al’umma, majalisar ta dora ma kanta alhakin kula da wadanda suka mutu, shi ya sa muka gyara makabartar Ikorodu kamar yadda kasashen duniya suka yi.
“Zan tabbatar da cewa an samar da matakan tsaro da suka dace, tare da yin tir da duk wanda ya aikata wannan haramtacciyar dabi’a a makabartar. “Mun yi gyare-gyare da yawa, inda muka haskaka makabartar da na’ura mai amfani da hasken rana, da samar da tsarin ruwa da kewaye makabartar.”
A halin da ake ciki, daya daga cikin masu gadin makabartar, Nurudeen Lawal, ya ce sun yi artabu da wanda ake zargin kafin a kama shi da misalin karfe 1:30 na dare, dauke da buhu cike da sassan jikin dan adam a lokacin da yake kokarin tserewa.
“Muna gudanar da aikin sa ido a makabartar akalla sau uku zuwa hudu a wani yunkuri na lura da zagayen makabartar. Nan da nan sai muka fara jin motsi, da isarmu sai muka ga wanda ake zargin dauke da buhu, sai muka kalubalance shi kan yadda ya shiga da aikin da ya yi a makabartar”.
“Lokacin da muke yi masa tambayoyi, mun bukace shi da ya bude buhunsa, ya ki, hakan ya haifar da fada, da kokarin yin amfani da makami wajen tsoratar da mu domin ya gudu. Daga nan ne muka kama shi muka kai shi ofishin ‘yan sanda da sassan jikin domin ci gaba da yi masa tambayoyi,” in ji Lawal.