
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani direban mota mai shekaru hamsin da bakwai bisa zarginsa da daba ma matarsa wuka har lahira a karamar hukumar Gombi da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Suleiman Yahaya Nguroje, ya bayyana cewa, wanda ake zargin, Muhammed Alfa, mazaunin kauyen Lande B ne a karamar hukumar Gombi, an kama shi ne a ranar Asabar, day ga Janairu wannan shekara ta 2022, bayan da ya daba ma matar sa, Hamsatu Muhammad ‘yar shekara 40 wuka.
Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake zargin yana da ‘ya’ya takwas tare da matar da ta rasu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kafin faruwar lamarin, wanda ake zargin ya saki wannan mata da ta rasu, amma marigayiyar wadda ta koma wani gida da ke kusa da gidan shi,ta zo gidan tsohon mijin nata ne inda ta yi kokarin cire kyauren wata kofa don ta gyara sabon gidanta, inda aka kama ta, yayin da cikin haka ne kuma wanda ake zargin ya daba mata wuka ta mutu har lahira.
“cikin fushin abin da ta aikata, wanda ake zargin ya yi amfani da wuka ya daba ma matar tasa da ya saki, kuma mahaifiyar ‘ya’yansa wuka a wuya, sakamakon haka sai ta fadi kasa a sume,yayin da aka garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.”
“’Yan sanda sun kama wanda ake zargin aka kai shi hedikwatar ‘yan sanda reshen Gombi,bayan rahoton da aka samu daga wani mutum Jauro Babangida Boka, hakimin kauyen Lande,” in ji shi.
PPRO ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Ahmed Barde, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin tare da gaggauta gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu domin ya zama darasi ga wasu.