
‘YAN FASHIN FASHIN DAJI SUN TOSHE HANYAR TSAFE ZUWA GUSAA
A wani farmaki a tsakanin kauyen Karazau fa Gifan Kaura jiya Lahadi, ‘yan fashin daji sun toshe hanya Tsafe zuwa Gusau.
Majiyarmu ta Katsina Beat ta ruwaito cewa, ‘yan fashin dajin sun toshe hanyar ne don hana masu ababen hawan sanar da jami’an tsaro a garin Gusau a jihar ta Zamfara, a harin da ya rutsa da kauyukan da suke jusa da Jami’ar Gwamnatin tatayya dake Gusau.
Bashir Isa Gusau ya bayyana cewa, ‘yan fashin dajin sun jibge wasunsu a bisa hanya suna tilasta ma motoci fakatawa. ” ina kan hanya ta da yamma, sai aka shedaani cewa in dakata domin ‘yan fashin daji sun toshe hanya, yayin da daga bisani sai ga wasu motoci sun fara fitowa daga Gusau, inda suka bayyana cewa,an bude hanya, amma ‘yan fashin dajin suna nan suna kauyen Karazau.
Wani muyumen tsafe Abu Bala da yake aiki a Gusau ya ce, ” ‘yan fashin dajin sun bar wajen a lokacin da ya iso kauyen, amma akwai dimbin mutane da motoci da suka shaida masa cewa, yan fashin suna cikin kauyen” ya jara da cewa, kauyen Karazau yana tsakanin Jami’ar tarayya ne da ke Gusauda da shingen bincike na ‘yan sanda.
- Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara Muhammad Shehu ya ki ya ce komai a yayin kiransa ta waya haka kuma bai bayar da amsa ba, a lokacin da aka aike masa da sakon kar ta kwana.