‘ Yan bindigar dajin da ake zargin fulani ne masu satar shanu, garkuwa da mutane gami da kisan ba gaira da suka kashe hakimin ‘Yantumaki marigayi Abubakar Atiku Maidabino sun shiga komar ‘yansanda kamar yadda Kakakin rundunar SP Gambo Isa ya tabbatarwa manema labarai su.
Idan za’a tuna su waxannan ‘yanbindiga sun je gidan hakimin acikin watan Yunin shekarar 2020 inda suka fara kashe xaya daga cikin masu gadin gidan hakimin mai suna Gambo Isa kafin daga karshe suka isa suka kashe shi hakimin.
Kamar yadda xaya daga cikin su da ya shigo hannu mai suna Yusuf Abdullahi mazaunin garin Kagara dake qaramar hukumar Matazu ya ce, sun je garin tare da wasu da ake nema har yanzu, wato, Shamsu, Ibrahim, Salmanu da kuma Kabir inda suka yi wannan aika-aika.
Hakimin wanda yake qarqashin qaramar hukumar Xanmusa ne, qaramar hukumar dake xaya daga cikin qananan hukumomin dake fama da aiyukan ta’addancin varayin daji dake Jahar Katsina.
Qarin bayani na nan tafe