
Read Time:34 Second
‘Yan bindiga a yankin Maru da ke jihar Zamfara sun sako yara uku da su ka sace da sauran mutane wajen wata hudu da su ka wuce.
Rahoton ya nuna ‘yan bindigar sun sako yaran ba tare da karbar kudin fansa ba biyo bayan wata yarjejeniya tsakanin su da manoma a yankin.
A kan samu wasu yankuna da ‘yan bindiga ke shafawa wasu sassa lafiya don kulla wata yarjeniya.
Wannan na nuna zuwa yanzu gagarumin matakan da a ke dauka da zummar murkushe barayin bai gama kai wa ga gaci ba.
Baya ga babban birnin jihar Zamfara Gusau, sassan jihar na cikin yanayin datsewar sadarwar salula don samun damar kofar rago ga barayin.