
A kalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu a harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu da ke kananan hukumomin Igabi da Chikun da Zangon-Kataf a jihar Kaduna, yayin da aka yi garkuwa da wasu sha takwas a Udawa, kan hanyar Birnin Gwari daga Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar hakan a ranar Lahadin da ta gabata,amma bai tabbatar da sace mutanen ba.
Wani shugaban al’ummar Udawa, Muhammed Umaru, ya bayyana cewa, an kashe mutum daya tare da yin garkuwa da sha takwas a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari Angwar Zalla a kauyen da sanyin safiyar jiya Lahadi.
Umaru ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 12:30 na ranar Lahadin, inda suka yi garkuwa da mutane sha takwas da suka hada da matan aure, manya da ‘yan mata.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi, yana mai cewa har yanzu wadanda suka sace mutanen ba su tuntubi iyalan wadanda aka sace ba, ko kuma shugabannin al’umma.
A halin da ake ciki, kwamishinan, a sanarwa daban-daban da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce al’ummomin da abin ya shafa da suka hada da Angwar Zalla da Kerawa da Ungwan Rimi-Afana Road da Sabon Garin Ungwar Dalha, na karkashin kulawar jami’an tsaro.
A cewar Aruwan, “Hukumomin tsaro sun kai rahoto ga gwamnatin jihar Kaduna cewa, mutane hudu sun mutu, daya kuma ya jikkata, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Kerawa, karamar hukumar Igabi.”
Kwamishinan ya kara da cewa, “A cewar rahoton, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen, inda suka yi ta harbe-harbe, sannan suka kashe mazauna garin guda hudu, wadanda aka bayyana sunayensu da; Lado Shuaibu da Usman Haruna da Ayuba Muntari da Jafar Abdullahi.
“An bar Mallam Mamuda da rauni, yayin da ‘yan fashin suka yi awon gaba da wasu babura da kayayyakin jama’a.
“A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan matafiya a kan hanyar Ungwan Rimi zuwa Afana a karamar hukumar Zangon Kataf. Wani Joshua Kawu ya samu rauni a kirjinsa, inda aka garzaya da shi asibiti, daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.”
A wata sanarwa da Aruwan ya fitar ya ce, “Hukumomin tsaro sun kai rahoto ga gwamnatin jihar Kaduna cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu a wasu hare-hare biyu da suka faru a kananan hukumomin Igabi da Chikun.
“A cewar rahoton, ‘yan bindiga sun kai farmaki Sabon Garin Ungwar Dalha, wani kauye da ke wajen unguwar Maraban Jos, a karamar hukumar Igabi.
“’Yan bindigar dauke da makamai sun kai hari kauyen inda suka shiga wasu gidaje,sannan suka rika harbin iska. Wata matar aure mai suna Hadiza Mohammed ta sami harbin bindigar, kuma ta mutu nan take.“A karo na biyu, ‘yan bindiga sun kai hari Ungwan Zallah a Udawa, karamar hukumar Chikun, kuma an harbe wani Moses Jaja har lahira.“Gwamna Nasir El-Rufai ya samu rahotannin a cikin yanayi na bakin ciki, kuma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda da aka kashe a hare-haren da aka kai a kananan hukumomin biyu. Ya yi wa wanda ya jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa yayin da yake jajantawa al’ummomin da aka kai harin.”A halin da ake ciki, kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ASP Muhammed Jalige,bai yi nasara ba.