
Da yammacin jiya Litinin wasu ‘yan bindiga a Yola babban birnin jihar Adamawa sun shiga wani asibiti inda suka yi awon gaba da mai Asibitin.
Wanda aka sacen, Dokta Saidu Bala, shi ne tsohon Darakta na asibitin kwararru na Yola.
Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun mamaye asibitin ne bayan karfe 6 na yamma, a daidai lokacin da mazauna unguwar suke yin sallar Magariba.
Majiyar ta ce da isarsu asibitin, sai suka yi ta harbe-harbe don tsoratar da mutane.
“‘Yan bindigar sun kai farmaki asibitin jim kadan bayan sallar Maghrib inda suka yi harbin cikin iska don tsoratar da mutane.”
“Sai suka je ofishin Dakta Sa’idu Bala suka tafi da shi. An gudanar da wannan ta’addanci cikin gaggawa kasa da mintuna biyar,” kamar yadda aka tabbatar ma da majiyarmu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar wa jaridar Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin zakulo maharan tare da kubutar da wanda aka sace.
“Mutanenmu sun gano harsashi guda uku da aka yi amfani da su a inda aka yi wannan aiaka-aika, kuma nan take mun tura jami’an yaki da garkuwa da mutane domin ceto likitan da aka sace,” inji shi.
Wannan Lamari dai ya faru a daidai lokacin da ake fargabar akan tabarbarewar matsalar tsaro a kasar, musamman a arewacin kasar.