Read Time:39 Second
Akalla mutane hudu ne suka mutu yayin da wasu suka samu raunuka a wani hari da aka kai kauyukan Dugara, Daurawa da Gidan Gadi duk a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da karfe 10 na daren Juma’a a cewar mazauna garin.
Usman Ibrahim, wani mazaunin Yarkirya ya ce ‘yan bindigar sun mamaye kauyukan da manyan makamai tare da lalata gidaje da dama.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar SP Gambo Isa ya ce ba su da labarin harin.
Ya ce hakan na iya kasancewa sakamakon rashin tsarin sadarwa a yankin da harin ya faru.
Sai dai Mista Isa ya bada tabbacin zai yiwa jama’a bayanin gaskiya ko akasin haka da zarar ya tabbatar da ikirarin.