
Wasu ’yan daba sun kai farmaki ofishin wani gidan jarida ta yanar gizo da ke Gusau a daren Litinin da ta gabata,a ofishinsu na jihar Zamfara a kokarinsu na koya wa daya daga cikin ma’aikatan, Abdul Balarabe darasi mai gauni.
A cikin wata sanarwa da gidan rediyon mai suna ‘Thunder Blowers,’ ya fitar, ya bayyana cewa, “‘yan ta’addan sun ce an aiko su ne ga daya daga cikin ma’aikatannmu wanda yake ba ya nan, sai suka zabi su lakada wa ma’aikatan da ke wurin duka, inda suka jikkata Mansur Rabe, editan yada labarai.
Tare da lalata wasu kayan aikinmu.” Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ‘yan barandan sun tafi da wayar Rabe da wata kwamfutar tafi-da-gidanka na wani ma’aikaci mai suna Sulaiman Dan Aljanna.
Duk da haka, gidan yada labaran ‘Thunder Blower’ ya ce, ba su da masaniyar wanda zai iya aika ‘ yan bindiga a kan irin wannan manufa.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton da majiyar tamu ta yi, ba a sami jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu ba.