
Kamishinan muhalli na jihar Kogi ya ketare rijiya da baya a wani harin da masu garkuwa da mutane suka kai masa.
Chief Victor Adewale Omofaiye ya kubuta dagayunkurin sace shi ne a ranar Lahadin nan a tsakain kauyukan Oke-Ijumu da Iyara dake karamar hukumar Ijumu.
Shedar gani da ido da aka sakaya sunansa ya bayyaya cewa, wannanlamari ya da misalin karfe biuar na yammacin ranar ta Lahadi, a bisa hanyarsa ta dawowa bayan da ya baro garinsa na haihuwa na Ekinrin Adde, inda ya halarci wasu bukukuwa. Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanensun yi awon gaba da wasu matafiya.
Kwamishinan ya bayyana ma wakilin gidan rediyon jihar dake Lokoja cewa, ” wasu mutane da ba tantance su ba da yawansu ya kai ashirin dauke da bindigogi, sunyi mana kawanya.”
A cikin hanzari dogarinsa ya dauki mataki na gaugawa ya kubutar da shi, shi kuma ya sam raunin harbin bindiga a kafarsa.
Basraken Ekinrin, Oba Anthony Bamigbaiye Idowu ya tabbatar da faruwar wannan lamari, a wani takitaccen sako da ya aike.
Duk wani yunkuri jin ta bakin mai magana da yawun ‘yansanda na jihar ta Kogi, William Ayah ya ci tura.
Dukkokarin da wakilinu ya yi na samun yin magana da kwamishinan ya ci tura, sakamakon watarsa bata Shiga.