
Tsohon shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Mohammed Dikko Umar ya shaidawa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Larabar da ta gabata cewa, ya sayi kadarori na kimanin Naira biliyan hudu da dubu dari bakwai(4.7) tare da kadarori da ya samu ta hanyar horarwa da kuma aikin tuka mafi yawan shugabannin kasashen Afirka a tsawon shekarun da ya yi yana aiki.Air Marshal Dikko Umar ya bayyana haka ne a lokacin da ake ci gaba da shari’ar zarge-zargen da ake yi masa na halasta kudaden haram da almundahana a gaban mai shari’a Nnamdi Dimgba na babbar kotun tarayya da ke Abuja.A ci gaba da yi masa tambayoyi da lauya mai shigar da kara, Sylvanus Tahir ke yi. Dikko ya ce; “Shekaru talatin da shida da na kwashe na bautar ubangijina, na yi aikin tuka jirgin shugaban kasa na tsawon shekaru goma sha bakwai. Yawancin tafiye-tafiyen a wajen Najeriya ne, kuma na yi tafiye-tafiyen horo da yawa a wajen kasar.”A wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC Wilson Uwujaren ya fitar, ta ruwaito Dikko na bayyana cewa, ya tuka dukkan shuwagabannin kasashen Afrika a tsawon shekarun da ya yi na aiki, in banda shugabannin Cote D’Ivoire da Togo.“Na samu makudan kudade masu yawa, na yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.Ina da gonaki biyu da kuma fili kimanin hekta 17, a Abuja,da kuma biyu a Kaduna s hekta hudu da kuma hekta 200 daidai. Ni manomi ne a tsawon rayuwata.” Da aka tambaye shi dalilin da ya sa bai ba kotu wasu takardu da za su tabbatar da ikirarin da ya yi game da wadannan kaddarori ba? Sai ya ce “babu wanda ya nemi ya yi hakan”. Sai dai ya kara da cewa, ya bayyana hakan a cikin bayanin da ya yi ga EFCC.Dikko ya kuma shaidawa kotun cewa, “rundunar sojin saman Najeriya tana da nata tsarin aiki”; ya kara da cewa aikin ba shi da tsarin biyan kuɗi ta hanyar Intanet a lokacinsa.Sai dai wasu bayanai da aka gabatar a gaban kotu sun nuna cewa lokacin da Dikko yana aiki, ya karbi albashin sa ta banki. Hakanan,a daftarin da aka gabatar, shafuffuka na 22 zuwa 472, suna nuna fitar da kudade ta hanyar zamani watau ‘e-transactions’na wasu jami’an da ba a lissafa ba.Kuma wannan mu’amala ta fitar da kudade ta faru ne a watan Agustan 2012,a lokacin wanda ake tuhuma yana Babban Hafsan Sojan Sama.Sai dai sanarwar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar ta ce, mai shari’a Dimgba ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 1 ga Maris, 2022, domin karbar jawabai na karshe daga lauyoyin da ke shari’ar.An fara shari’ar Dikko ne a ranar 25 ga watan Junairu, 2017, a kan tuhume-tuhume 7 da suka hada da halasta kudaden haram da kuma mallakr kudi har Naira biliyan 9.7. An yi watsi da Shida daga cikin tuhume-tuhumen sakamakon gabatar da tuhumar da babu tabbas .