
An jibge sojojin Sudan kan iyakar kasar da Habasha da ake takaddama a kai.
Sojojin sun sanar da cewa suna da cikakken iko da yankin da ake kara takun saka tsakanin kasar ta Sudan da Ethiopia.
A ranar 1 ga watan Disamba ne sojojin Sudan suka sanar da tarwatsa tare da karbe ikon wani matsugunin Habasha a yankin al-Fashaga da ake takaddama a kai.
Sanarwar ta biyo bayan rahotannin da ke cewa an kashe sojojin Sudan 21 tare da jikkata wasu 30 a wata arangama da dakarun Habasha a Birkat Nourain a yankin da ake takaddama a kai kwanaki hudu da suka gabata.
Bayan arangamar, shugaban mulkin soji na Sudan, Laftanar Janar Abdel-Fattah al-Burhan, ya sha alwashin cewa kasarsa ba za ta mika wa kasar Habasha ko taki daya ba.