
Read Time:21 Second
Sojojin Najeriya sun kama wasu ‘yan bindiga da suka jikkata a wata cibiyar kula da lafiya a jihar Zamfara.
Kafar yada labarai ta PR Nigeria,ta ruwaito cewa,‘Yan ta’addan da aka cafke na daga cikin wadanda suka tsere daga harin sama da jirgin sojin Najeriya na Air Component na Operation Hadarin Daji ya kai a sansanin na ‘yan ta’adda a jihar ranar Juma’ar da ta gabata.