
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kwara, Reverend Paul Olawoore, ya rasu.
Shugaban ya rasu ne a jiya Asabar, 1 ga watan Janairu, 2022 yana da shekaru 60 a duniya.
A halin da ake ciki, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jajantawa al’ummar Kiristocin jihar bisa wannan rashi.
Gwamnan a cikin sakon ta’aziyyar ya bayyana rasuwar shugaban ha CAN a matsayin mai raɗaɗi.
“Hakika rashi ne mai zafi na fitattun limamai da suka sadaukar da rayuwarsu gaba ɗaya ga bautar Allah da ɗan adam. Za a yi kewarsa a matsayin limami mai ƙwazo da aka sani da neman zaman lafiya da ƙauna ga kowa.
“Ina mika ta’aziyyata ga iyalansa da ‘yan Katolika da daukacin Kiristocin Jihar Kwara kan wannan babban rashi. Ya yi fatan Ubangiji Allah ya hutar da shi, ya kuma yi wa iyalai da al’ummar da ya bari baya ta’aziyya,” a wata sanarwar da ke dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye.