
Shugaban kasar Somaliya, Mohamed Abdullahi Mohamed ya dakatar da firaminista Mohamed Hussein Roble daga mukaminsa sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa da aka yi masa.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Villa Somalia, ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, 26 ga watan Disamba, an zargi Roble da yin katsalandan a binciken da ake yi na kwace filaye.
“Shugaban ya yanke shawarar dakatar da Firayim Minista Mohamed Hussein Roble, tare da dakatar da ikonsa bayan da aka alakanta shi da cin hanci da rashawa”.
Dakatar da Roble daga karagar mulki ya zo ne bayan cacar baka da ta gudana tsakanin bangarorin biyu a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka zargi juna da gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da ya gudana.
Sanarwar da shugaban ya fitar ta ce, “sun shiga cikin maganar ne saboda zargin almundahana da almubazzaranci da dukiyar al’umma, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano zarge-zargen, an dakatar da ikon Firayim Minista har sai an gudanar da bincike.”