
SHUGABAN ƘASA YA YI TA’AZIYYA TARE DA KARRAMA MARIGAYI BRIG. GEN. DZARMA ZURKUSHU DA SAURAN MUTUM 6 DA SUKA RASU.Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zurkushu da wasu ’yan kishin kasa su 6, wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare Askira-Uba a harin da aka kai jihar Borno a farkon watan nan.
Shugaban wanda ya yi magana ta bakin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a wajen bikin jana’izar ‘yan kishin kasar wanda aka gudanar a karamar hukumar Gibson Jalo da ke Yola a jiya 26 ga watan Nuwamba, ya kuma nuna jin dadinsa dangane da irin ƙundubalar da marigayin yayi tare da abokansa don kare kasa, ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa iyalansu haƙurin rashinsu.
A bisa wannan sadaukarwar da hafsoshi na soja suka yiwa kasa dan kare ƙasarsu ta gado, Gwamnan jihar Adamawa Rt Hon Umaru Ahmadu Fintiri ya canza wa shahararriyar titin Lagas road da ke Yola da sunan Marigayi Birgediya Janar Dzarma Zurkushu.
Baya ga gudunmawar Naira Miliyan 10 ga iyalan marigayi Birgediya Janar Zurkushu da kuma wasu Naira Miliyan 17 ga iyalan sauran jaruman shida da suka rasu. Gwamnan ya kuma bayyana marigayi Janar a matsayin kwararre, mai tawakkali da sadaukar da kai, Gwamnan ya kuma bayar da umarnin kafa tutar kasa a jihar na tsawon kwanaki 3 domin karrama jaruman da suka mutu.
A nasa jawabin tun da farko a wajen taron da ya halarta, COAS Laftanar Janar Faruk Yahaya, wanda ya mika tutocin kasar ga ‘yan’uwa na manyan hafsoshi da suka rasu, ya yi addu’ar Allah ya jikan su da rahama.
Ya kuma tabbatar wa da iyalansu cewa hukumar NA za ta gaggauta aiwatar da dauke nauyin ayyukan da jaruman suka mutu suna yi musamman ga baiwa ‘ya’yansu tallafin karatu.
COAS ta bayyana godiya ga shugaban kasa da sauran wadanda suka halarci jana’izar don girmama masu kishin kasa.
Kafin ƙarƙarewa, an gudanar da addu’o’i na musamman a cocin St Stephen’s Military Church (Prot) da kuma babban masallacin Juma’a na Gibson Jalo Cantonment, inda aka yi addu’o’in neman gafarar wadanda suka mutton.