
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Oyo, da iyalan gidan sarautar Ibadan da kuma al’ummar masarutar Ibadan bisa rasuwar Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji.
Shugaban a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa,Femi Adesina ya fitar, ya tabbatar da cewa marigayi Kabiyesi shugaba ne mai hangen nesa, kuma mai tausayi, wanda ya yi amfani da tasirinsa a matsayinsa na mai martaba sarkin gargajiya, kuma mai kaunar masana’antar kere-kere wajen ciyar da al’ummarsa gaba,tare da kwadaitar da su da kuma zaburar da su wajen bayar dagudunmuwarsu wajen gudanar da ayyukansu da kuma na al’umma.
Yayin da rasuwarsa ta bar wani babban gibi da zai yi wuya a cike shi. Shugaba Buhari ya bukaci al’ummar Ibadan da ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban da su girmama marigayin ta hanyar koyi da kyawawan dabi’unsa na karamci da zaman lafiya, juriya da sadaukarwa.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da jana’izar Olubadan na kasar Ibadan na 41, shugaban kasar ya ce, ya yi imanin cewa tsarin zaben wanda zai gaje shi za a yi shi ne ta hanyar hikima da kyakkyawar fahimta wacce ta nuna irin rayuwar da sarkin ya yi.
Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya hutar da Oba Adetunji ya kuma baiwa iyalai da abokan arziki hakurin rashinsa.