
Kasar sanagal ta yi kira ga kasar Sin da ta tallafa ma kasashen yankin Sahel a yunkurin su na yaki da ta’addanc. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN)ya ruwaito cewa,
Ministan harkokin wajen Senagal, Aissata Tall Sall, ta bayyana haka a lokacin da ta gana da takwararta ta kasar Sin, Wang Yi a birnin Dakar, a taron da aka yada ta yanar gizo. Ta ce, “ a wani bangare na hadin guiwa a yankin Sahel, muna bukatar muryar kasa Sin, duba da tasirinta, ta zama babbar murya ta nuna goyon baya ga kasar Senegal.
Haka kuma ta yi kira ga dukkan sauran kasashen da ke da hannu a yaki da matsalar rashin tsaro a yankin Sahel, domin dakarun kasar , su sami karin hanyoyin doka, don yakar ‘yan ta’adda da rashin gaskiya.”
Ministan harkokin wajen Senegal ta ce,” kasar Sin ta riga ta zuba jari a wasu fannoni ,kamar aikin gona, kiwon lafiya, al’adu, ababen more rayuwa, wasanni da sauran sassa na tattalin arzikin Senegal.”
Ministan ta bayyana fatan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zai amfani al’ummomin kasashen biyu.
Yankin Sahel dai ya shafe shekaru yana gwagwarmayar yaki da ta’addanci. A cikin shekarar 2014, Faransa ta kaddamar da wani shirin yaki mai take ‘ Operation Barkhane’ don taimakawa kasashen yankin.
A watan Yunin 2021, duk da haka, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ba da sanarwar shirin dakatar da aikin nan da kwata na farkon shekarar 2022, yana mai bayyana cewa za a yi kokarin kasa da kasa don taimakawa yankin yakar ta’addanci a maimakon haka.