
Read Time:36 Second
Kakakin rundunar sojan kasan Najeriya Onyema Nwachukwu ya ce sam bai fitar da labarin gargadin sojoji su guji yin juyin mulki ba.
Nwachukwu na martani ne ga wata kafar labarun yanar gizo da ta ruwaito shi ya na gargadin.
Onyema Nwachukwu ya ce ba mamaki kafar labarun ce ita kadai ba ta san cewa ba shi da hurumin magana a madadin cibiyar tsaron soja ba don shi matsayin da na iya rundunar sojan kasa ne.
Hakanan kakakin ya ce ai ba bukatar gargadin soja kar su yi juyin mulki ba don ba a kokonton da’ar su ga shugabannin farar hula.
A nan Nwachukwu ya zaiyana labarin da karya zalla ga labarin da ba shi da tushe bare madafa.