Wani direba da a tantace kowanene ba Abuja, ya rasa ransa bayan da ya kai ma wata bishiya karo a yayin da yake tuki.
Hadarin ya afku ne a kan babban titin Shehu ‘Yar Adua, da yammacin ranar Juma’a.
An bayyana cewa , motar kirar Hyundai Sonata na sheka gudu ne, a lokacin da hatsarin ya afku.
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa kafar yada labarai ta ‘THE WHISTLER’ cewa, direban motar, ya rasa yadda zai tafiyar da motar ne,sannan ya kauce hanya, zuwa wani bangaren, kafin ya bugi wata bishiya.