
Read Time:34 Second
Dan tsohon shugaban Libya marigayi Moammar Ghaddafi wato Saiful Islam ya aiyana shiga neman takarar shugabancin kasar.
Hukumar zaben Libya ta tsaida ranar 24 ga watan gobe a matsayin ranar zaben shugabancin kasar ta Afurka ta arewa.
Saiful Islam na cikin na kan gaba a jerin masu neman shugabancin kasar da su ka hada da Kwamandan gwagwarmaya na gabashi Khalifah Haftar, firaminista Abdulhamid Al-Dheibah da kakakin majalisa Aguila Saleh.
An ga Saiful Islam da farin rawani da farin gemu ya na cika takardar tsayawa takara a garin Sebha na kudanci.
Duk da mara baya ga gudanar da zaben da kasashen duniya ke yi, ba tabbas na lalle zai iya samun nasarar gudana.