
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Yobe ta bayyana cewa, karya brojojin Najeriya suka tabka, basu ceto ‘yan sandanta guda ashirin ba daga hannun masu garkuwa da mutane ba kamar yadda sojojin su ka yi ikirari.
Mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar tsaron, Birgediya Janar Bernard Onyeuko,ya bayyana wancan furuci a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis da ta gabata. Ya ce, dakarun Operation Hadin Kai, sun ceto ‘yan sanda 20 da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su.
Ya ce, “A dunkule, an kashe ‘yan ta’adda 62, sannan an kama 28 daga cikinsu, sannan an kwato makamai iri-iri 54 da alburusai 144 daban-daban. Haka kuma, an kwato jimillar dabbobi 101 da aka yi garkuwa da su, da kuma jami’an ‘yan sanda guda 20 da aka yi garkuwa da su, wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari a ofishin ‘yan sanda. Ya ce,sojojinsu a Buni Yadi ne suka kubutar da su a cikin wannan lokaci.”
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan maganar ‘garkuwa da kwatowa’ a matsayin karya da yaudara.Sanarwar ta kara da cewa, “An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ne akan yadda labarai ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuni da cewa, ‘yan sanda ashirin (20) da mayakan Boko-Haram/ISWAP suka yi garkuwa da su a yayin wani hari da aka kai a ofishin ‘yan sanda na Buni-Yadi da ke karamar hukumar Gujba a jihar, dakarun sojojin Nijeriya (Operation Hadin Kai) sun ceto su.”“Abin takaici ne a lura cewa an buga wannan labari na karya a kafafen yada labarai da yawa, ba tare da neman karin haske daga hukumomin ‘yan sanda da aka bukatar ba.“Abin da ya fi daukar hankali shi ne ana zargin irin wannan labarin ya fito ne daga majiyoyin soja. “Saboda haka, rundunar ‘yan sandan tana son ta nanata kamar haka: “Labari kan zargin sace ‘yan sanda 20 a Buni-Yadi tare da kubutar da su da sojoji suka yi, yaudara ce, kage-kage ne, kuma labarin karya, domin ba a yi garkuwa da ko dan sanda daya tilo daga garin Buni-Yadi a ranar da lamarin ya faru ba, ko ma; A ranar Talata 30 ga Nuwamba, 2021, wasu da ake zargin mayakan Boko-Haram/ISWAP sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Buni-Yadi a karamar hukumar Gujba. Yankin jihar tare da kona gine-ginen, amma ba a samu asarar rai ba, ko wani dan sanda da aka yi garkuwa da shi, ko kuma aka bayyana bacewarsa.