
Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da cewa, wani harin da ta kai ta sama a jiya Asabar, 1 ga watan Janairu wannan sabuwar shekar, ya kashe shugabannin ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo watau Alhaji Auta da Kachalla Ruga, a wani dajin jihar Zamfara.
Jami’in hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Cdre Edward Gabkwet, ne ya tabbatar ma majiyarmu da hakan a jiya Asabar.
A wani lokaci, jaridar LEADERSHIP ta ruwaito rahoton kashe shugabannin ‘yan ta’addan daga majiyoyin tsaro.
Shahararrun shugabannin ‘yan fashin sun gana da ‘yan ta’addan ne bayan da wani jirgin saman sojan saman Nijeriya, karkashin rundunar Operation Hadarin Daji, da ke aiki da sahihan bayanan sirri ya kai farmaki a dajin Gusami da kauyen Tsamre da ke karamar hukumar Birnin Magaji a jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Har ila yau jerin hare-haren ta sama sun kashe mayakan ‘yan bindiga a yankin.