
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama jimillar mutane dari tara da casa’in da tara da ake zargi da aikata laifuka dari shida da takwas (608) a shekarar nan mai karewa ta 2021.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sufeto SP Isah Gambo ne ya bayyana hakan a madadin kwamishinan ‘yan sandan, AIG Sanusi Buba yayin taron manema labarai na karshen shekara da aka gudanar a ofishin rundunar a ranar Alhamis.
SP Gambo a wajen taron ya yi karin haske game da kamen da aka yi a shekarar da ke Mareham.
Ya ce, “jimillar mutane dari takwas da saba’in da hudu na wadanda ake zargin suna fuskantar shari’a a kotunan shari’a daban-daban na jihar.”
“Ya kuma bayyana cewa an kama jimillar mutane dari da hamsin da bakwai da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, an kuma gurfanar da wadanda ake tuhuma dari da arba’in da biyar zuwa kotu yayin da ake ci gaba da bincike kan wadanda ake tuhuma goma sha biyu .
Kakakin ‘yan sandan ya kuma bayar da “ jimlar adadin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da aka kama a cikin wannan shekarar da ake nazari a kansu, a matsayin mutum sittin da biyar , daga cikinsu an gurfanar da wadanda ake tuhuma sittin da uku a gaban kotu, yayin da saura biyu da ake tuhuma ake ci gaba da bincike a kansu.
Hakazalika SP Isah ya bayyana cewa, “An kama mutane dari biyu da arba’in da hudu wadanda ake zargin barayin shanu ne.
An gurfanar da wadanda ake zargi dari biyu da talatin a gaban kotu, yayin da ake ci gaba da bincike a kan mutum goma sha hudu.