
Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu ya bayyana alhini da jimami, dangane da rasuwar Alhaji Bashir Tofa tare da bayyana cewar, ba shakka yan Nijeriya sun yi rashi adalin dan siyasa mai hangen nesa da son talakawa.
‘Bashir Tofa dattijo ne a kalamansa da huldarsa, nayi hasara abokin shawara, mutum mai hikima da raha tare da maraba a tsakaninmu don sadar da sakon da zai amfani al’umma cikin adalci da gaskiya ga kowane bangare na kasarnan” Inji Iyorchia Ayu
Ya nemi al’ummar jahar Kano da na Arewa da kasa baki daya dasu sanya iyalai da ‘yan uwan Marigayi Tofa cikin addu’oinsu sakamakon wannan rashin mai girma na dattijo, zarumi, dan kishin kasa, mutum mai taimakon al’umma da tsare gaskiya a zantukansa da hulda da kowa, musamman daga cikin yan siyasa Nijeriya.
Dr. Ayu ya bayyana Marigayi Tofa da kasancewa namijin duniya da bai da fargaba, ga bayyana abin da ya dace da aikata hakan gaban kowa don ciyar da al’ummarsa da kasarsa a gaba tare da neman hadin kai.
Baya ga gabatar da ta’azziyarsa ga iyalai da sauran ‘yan uwa da masoya al’ummar Nijeriya, ya kira tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Alhaji Umar Ghali Na Abba don sadar da sakon ta’azziya, da rokon Allah Ya gafarta masa da mafificiyar rahama a kabarinsa.