
Tare da: Rahoton NAN
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jiya Talata a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja lokacin da ya karbi bakuncin Janar Victor Sheiman, babban hadimin shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko.
Bayan ya saurari jawabin maziyartan, shugaba Buhari ya ce: “Na gamsu da ci gaban da kuka samu a matsayin kasa.
“Za mu iya amfana da yawa daga abubuwan da kuka samu. Na lura da iyawar ku, kuma za mu tuntube ku a wuraren da za mu iya haɗa kai, da yin aiki tare, musamman a fannin noma.
“Muna da ƙasar noma da yawan jama’a, kuna da fasaha, kuma tabbas za ku ji daga gare mu.”
A baya Sheiman ya yaba wa shugaba Buhari a kan aiki da yake domin amfanin al’ummar Najeriya, yana mai cewa haka ne shugaba Lukashenko ke yi a Belarus.
Ya kara da cewa: “Mu kasa ce mai kwanciyar hankali da kuma abokantaka, muna kokarin dogaro da kai a fannoni da dama. Za mu iya ba wa ‘yan Najeriya dama da yawa”.
“Za mu so mu hada kai a fannin masana’antu, noma, man fetur, matatun mai, ilimi, cinikayyar hadin gwiwa, sufuri,gina bututun mai da iskar gas, kera tayoyi da taraktoci da kuma kayayyakin tsaro, da dai sauransu.”
A cewar dan sakon na musamman, kasarsa ta isa noma sosai, kuma tana sayar da rarar kayan abinci da suka kai dala biliyan bakwai, duk shekara.
Ya kara da cewa kasar Belarus a shirye take ta hada kai da Najeriya a fannin noma na injiniyoyi, kuma za ta iya taimakawa wajen yaki da ta’addanci.