
A karo na farko naira ta fara tagazawa ko farfadowa a kasuwar canji a Najeriya bayan ta samu mafi koma baya a tarihi.
Zuwa rubuta wannan labari a na sayar da dala daya kan naira 540 a kasuwar canji bayan tun farko dalar ta kai naira 575.
Da alamun naira za ta cigaba da farfadowa don bincike ya nuna a na samun karancin masu bukatar dala don yanda tattalin arzikin jama’a ya samu koma baya.
Hakanan akalla yanzu an fara samun yabanyar gona inda mutane ke samun abinci daidai gwargwado daga dazukan Najeriya.
Za a cigaba da zuba ido kan yanayin canjin dalar da wani masani ya ce ya na hasashen zuwa karshen shekarar nan dala za ta koma naira 500 a kasuwar canji inda za ta koma naira 420 a canjin hukuma.