
Mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu shida suka jikkata, a wani hatsarin da ya rutsa da motocin haya uku a hanyar Sokoto zuwa Illela.
Mummunan hatsarin ya afku ne da safiyar Lahadin da ta gabata, a wani shingen bincike jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya suka kafa a kauyen Asara, kusa da kan iyakar Illela a jihar Sokoto.
Wani ganau ya shaida ma majiyarmu yadda lamarin ya faru, ya ce, motocin da abin ya shafa su ne,Toyota Avenses da Golf Salon,sun yi taho-mu-gama ne, a lokacin da suke kokarin kaucewa tsayawa wajen shingen binciken.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Daya daga cikin direbobin da ake zargin yana dauke ne da shinkafa da man kayan lambu day a fito daga garin Illela da ke kan iyaka, a kokarin da suke yi na kauce ma kamu, daga karshe ya shiga wani shingen binciken na kwastam da ke kauyen Asara.
“jami’an na kwastam sun dakatar da direban ne a yunkurin tsayar da motar domin bincike wanda hakan ya sa direban ya kasa tsaida motar, yayin da Motar ta ci karo da da ke shigowa, inda suka yi karo da juna yayin da dayar motar da ta zo daga baya ta yi karo da su biyun.
“Mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu nan take a cikin motoci biyu yayin da mutane akalla shida suka samu raunuka daban-daban a yayin hadarin.
Gungun jama’ar da suka fusata akan hasarar rayukan da aka yi sun kona motoci biyu na jami’an hukumar kwastam ta Najeriya da ake zargin su da haddasa wannan hatsarin.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Gwandabawa domin kula da lafiyarsu.”