
Read Time:18 Second
Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Muhammad Bello, ya kamu da citar Corona samfurin Omicrom. Ministan ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.ya ce, bayan jin rashin lafiya a ranar 28 ga Disamban da ya gabata, ya yanke shawarar zuwa gwajin COVID-19 a ranar Alhamis, kuma sakamakon ya zo masa inda ya nuna yana dauke da wannan cuta.