
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu ya bayyana a wajen taron bikin sauya shekar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gboko/Tarka, John Dyegh,daga jam’iyyarsa zuwa PDP cewa, Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, George Akume na kan hanyarsa ta komawa PDP.
Akume, wanda ya yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan jihar Benue a karkashin jam’iyyar PDP, a halin yanzu yana da gurin jagorantar jam’iyyar APC mai mulki.
Ayu ya kara da cewa, “Ku fara shirya takardun mika mulki kawai, domin PDP ta sha alwashin korar APC daga mulkin”
Ayu, ya kuma jaddada cewa ministan wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC a yankin arewa ta tsakiya, zai dawo jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya rasa komai.
“Bataccen danku,George Akume zai dawo PDP. Ina fadar haka ne bisa abin da na sani.”in ji Ayu.
“A baya na yi hasashen cewa, Akume zai rike tsintsiya, kuma ya rike; Yanzu ina tabbatar maku cewa zai dawo PDP. Idan ya dawo kar ku kyamace shi, amma ku tabbatar kun gyara shi, domin a inda yake a yanzu, ba a daidai yake tunani ba.”
Dangane da wanda ya sauya shekar kuwa, cewa ya yi, “Dyegh da magoya bayansa ’ya’ya ne da suka bace,wadanda suka gane hanya kuma suka koma gida.”
Shi ma da yake jawabi, Gwamna Samuel Ortom ya ce jam’iyyar APC ta gaza ta kowacce fuska, yayin da ya yi maraba da Dyegh da sauran magoya bayansa da dawowa cikin jam’iyyar PDP, tare da yi masu alkawarin yi masu daidai gwargwado.
Dyegh, ya ce ya dauki matakin sauya sheka daga APC zuwa PDP ne duk da cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa kawunsa ne, amma ya ga yadda Gwamna Ortom yake gudanar da manya-manyan ayyuka ne a jihar.