
Matasa daga kananan hukumomi bakwai da suka hada da masarautar Bauchi sun ziyarci fadar mai martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu.
Matasan dai na dauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban tare da rera wasu kalamai da ba a buga ba a yayin zanga-zangar.
Mai magana da yawun matasan Nurudeen Ya’u Gwabba a lokacin da yake zantawa da manema labarai ya bayyana cewa sun damu da cin mutuncin sarakunan Bauchi da Dass da wadanda ake zargin ‘yan asalin yankin Bogoro da Tafawa Balewa ne a makon jiya Juma’a a kan hanyarsu ta zuwa halartar taron.
Gwabba ya ce: “Muna alfahari da Sarkin Bauchi, haka kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar.Abin da aka yi masa babban wulakanci ne.
“Matasan Masarautar ba za su zauna kawai su nade hannuwansu suna kallon yadda ake musgunawa sarakunan da suke uban kowane irin kabila ba.
Hakazalika, Gamayyar Matasa da Dalibai na Jihar Bauchi sun yi kira ga gwamnatin Jihar Bauchi da ta kafa kwamitin bincike na shari’a domin gudanar da bincike kan harin da aka kai wa sarakunan Bauchi da Dass.
Gamayyar a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Usman Saleh, ta bayyana cewa “a hankali, ba za mu iya komawa cikin wannan ranakun da ake fama da rikicin kabilanci a jihar Bauchi ba saboda rikicin Tafawa Balewa na shekarar 1991 har yanzu yana cikin abubuwan tunawa.
Muna kira ga gwamnatin jihar da ta dauki matakin da ya dace domin babu wani mutum da ya kai jihar girma”.
A lokacin da yake karbar matasan a fadarsa, Sarkin Bauchi ya yi kira da a kwantar da hankula, inda ya shawarci matasan da su kame fushinsu, kada su bari ya tashi ya kai ga harin ramuwar gayya.
Sarkin wanda ya samu wakilcin Ajiyan Bauchi, Alhaji Abubakar Bala Ajiya, ya bada tabbacin cewa majalisar za ta duba bukatunsu tare da bayyana matsayar ta a lokacin da ya dace.