
Matar mai suna Shafa’atu ‘yar shekara 30,it ace wacce ta tsira daga harin ‘yan bindigar da ya yi sanadin mutuwar fasinjoji da dama, ciki har da ‘yan uwanta guda takwas.
Matar ta rasu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfordiyo da ke Sokoto, inda take jinya sakamakon raunukan da ta samu a harin da aka kai masu a ranar Litinin .
majiyarmu ta ruwaito yadda wata mota kirar ‘yan kasuwa da ke kan hanyar zuwa Kudancin kasar nan ta fuskanci hari a kan hanyar Sabon Birni zuwa Isa a Sakkwato.
Matar ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun bude ma motar tasu wuta.
Ta kara da cewa, bayan da ta yi bindiga ne sai ta fashe amma ‘yan bindigar sun tsaya domin kallon har yadda wadanda abin ya shafa suka mutu.
A cewarta, akwai dattijai 33 da yara da dama a cikin motar a lokacin da ‘yan bindigar da ake kyautata zaton masu goyon bayan Bello Turji ne, wani kasurgumin barayin da suke addabar yankin na Sakkwato suka kai harin.
“Sun yi ta harbe-harbe a kan motar mu har sai da ta murgina har sau uku sannan ta kama wuta. Ni da wani fasinja guda ne kawai muka fitodaga cikin motar, amma daga baya fasinjan ya mutu sakamakon raunin harbin bindiga,” inji ta.
“Na rasa ‘ya’yana hudu, mata uku duk sun girma da kuma jaririna mai watanni 10. Na kalle su, ciki har da mahaifiyata, kawun mahaifiyata, kanena da yayata sun kone kurmus yayin da maharan ke kallo suna murna.”
An yi jana’izar wannan baiwar Allah kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.