Masar da Saudiyya na neman hanyoyin da za su taimaka wa Libya ta samu kwanciyar hankali yayin da kasar da ke arewacin Afirka ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a mako mai zuwa.
A ranar Alhamis babban jami’in diflomasiyyar Masar Sameh Shukry da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan a birnin Alkahira sun ce, yana da muhimmanci a gudanar da zaben shugaban kasar Libya kamar yadda aka tsara.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa Shukry da Farhan sun bayyana cewa, “yana da muhimmanci a gudanar da zaben shugaban kasar Libya kamar yadda aka tsara”.
Zaben na da nufin taimaka wa hadin kan al’ummar kasar bayan shafe shekaru goma ana yakin basasa, ya kamata a gudanar da shi nan da mako guda kacal, amma ana ta kiraye-kirayen a jinkirta.
Kuri’ar da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Disamba, ita ce zaben shugaban kasar Libya na farko tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi da aka kashe fiye da shekaru goma da suka gabata.
Kusan shekara guda kenan zaben ya kasance ginshikin kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya a wannan kasa ta arewacin Afirka mai arzikin man fetur, kuma magoya bayansa na fargabar samun gurbi mai hatsari idan ba a gudanar da shi a kan lokaci ba.
Sai dai masu suka sun yi gargadin cewa, ci gaba da kada kuri’a a yanzu ka iya jefa kasar cikin wani sabon tashin hankali.