
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno (rtd) ya ce ayyukan Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da Islamic State in Greater Sahara (ISGS), suna karfafa gwiwar ta’addanci a yankin Sahel.
Don haka ya yi kira ga Malamai da masu wa’azi da limamai da su wayar da kan mabiyansu a kaa ta’addanci.
Ya ce, “Babu wata bindigar da ta fi wayewa da ilimi a matakin farko.”
Monguno ya shawarci malaman ne a jawabin da ya gabatar a wajen bude taron karawa juna sani karo na 14 na kungiyar malamai da masu wa’azi da limaman kasashen yankin Sahel a Abuja.
Ya ce ta’addanci da karuwar ayyukan ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayin addini a yankin Sahel ke yi tun daga shekarar 2016, kungiyar ISGS ce ke jagorantar ta, wadda mafi yawan lokaci take gudanar da ayyukanta a Mali har zuwa Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.
Ya ce ayyukan ta’addanci na kungiyoyi irin su Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM) da Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS ke karfafa ta’addanci, wadanda ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar yankin. .
Kungiyar Islamic State in the Greater Sahara (IS-GS) kungiya ce ta ‘yan ta’adda da ke bin akidar jihadi ta Salafiyya. An kafa kungiyar ne a ranar 15 ga watan Mayun 2015 bayan rarrabuwar kawuna tsakanin kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-Mourabitoun.