
Gwamnatin jihar Katsina ta dage takunkumin da ta sanya na amfani da tsarin sadarwar wayar salula a jihar.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kafa dokar ne watanni uku da suka gabata a wani mataki na dakile matsalar rashin tsaro.
kananan hukumomin da suka hada da: Jibia, Batsari, Safana, Kurfi, Danmusa, Dutsin Ma, Kankara, Matazu, Musawa,
Funtua, Faskari, Sabuwa, Dandume, Bakori, Danja da Malunfashi duk sun katse.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da mai baiwa gwamna Masari shawara kan harkokin tsaro, Ibrahim Ahmed Katsina, gwamnatin jihar ta ce ana samun zaman lafiya a yankunan.
“Yayin da nake magana da ku, an dawo da hanyar sadarwa a wasu kananan hukumomi.”
Ana sa ran gwamnatin jihar za ta fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba.