
Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin dunuya a jiya Talata ya samu sabbin mambobi biyar, yayin da Albaniya, Brazil, Gabon, Ghana da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka fara karbar mukaman da suka samu a zaben da aka gudanar a watan Yuni.
Gabon da Ghana kowanne ya kasance a kwamitin majalisar sau uku a baya, sannan hadaddiyar daular Larabawa sau daya. Kwamitin mai membobi 15 she ne kwamitin Majalisar Dinkin Duniya mafi karfi.
Kasashen Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya da kuma Amurka su ne mambobi na din-din-din, wadanda ke da karfin iko. Sauran mambobin Majalisar mai wakilai 193 ne ke zabar su na tsawon shekaru biyu wadanda yankunan duniya suka kebe.
Kujerun da ba na din-din-din ba a Nahiyar Africa sun hada da Kenya da Tunisiya da jamhuriyar Nijar.
A shekarar da ta gabata ne, shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Senegal suka yi kira da a samar da wakilci na din-din-din na al’ummar Afirka a majalisar.
Membobin majalisar kuma za su iya kiran tarurruka kan batutuwan da suka shafi tsaro.
Fiye da kasashe 50 daga cikin mambobi 193 na Majalisar Dinkin Duniya ba a taba zabensu a majalisar ba tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1946.