
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra,Encheng Echeng,ya yi kira da a hada kai tsakanin ‘yan sanda da ‘yan jarida.
Daily trust ta ruwaito cewa,Kwamishinan ya yi wannan kiran ne a jiya Larabar lokacin da shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta ‘Correspondents’ Chapel of Nigeria Union of Journalists (NUJ) reshen Anambra suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Amawabia, Awka ta kudu.
Ya ce ‘yan sanda da ‘yan jarida abokan hadin gwiwa ne wajen yaki da miyagun laifuka a cikin al’umma.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa ‘yan sanda na bukatar ‘yan jarida domin su samu damar yaki da miyagun laifuka domin ci gaban al’umma.
Ya ce yayin da ‘yan sanda ke neman ‘yan jarida da su rufe idanunsu ga matsalolin da suke fama da su,ya kamata su bayar da rahoto da idon basira domin amfanin jihar.
Tun da farko, shugaban kungiyar ‘yan jaridar, Cif Chuks Ilozue, ya yabawa kwamishinan bisa yadda ya kawo kwanciyar hankali a jihar tun bayan shigarsa ofis.