k
Jami’in yada labarai na karamar hukumar Bagwai Tasiu Jibo Dawanau ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kano.
Ya ce al’amarin bakin ciki ya yi sanadin mutuwar fasinjoji akalla biyar yayin da aka ceto wasu shida da ransu.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a madatsar ruwa ta Bagwai da misalin karfe 5 na yamma lokacin da mutanen suka shiga jirgin da injin daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai kuma ana cikin haka ya kife.
Jami’in yada labaran ya bayyana cewa a halin yanzu tawagar masu ninkaya, ‘yan kwana-kwana, NSCDC, ‘yan sanda da shugaban karamar hukumar suna aikin neman ceto a madatsar ruwan.
“Ya zuwa yanzu, an ceto mutane shida da ransu sannan mutane biyar sun rasa rayukansu. Tuni dai aka kwashe gawarwakin zuwa babban asibitin Bagiwa.
“Ana ci gaba da bincike amma zuwa gobe, ya kamata mu iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a cikin hatsarin,”
Majiya kanodaily