
Shugaban kungiyar masu fafitikar kafa kasar Biafra, Chika Edoziem ya haramta rera taken Najeriya a makarantu, tare kuma da sanar da haramta shanun Fulani a lokutan bukukuwa a yankin Kudu maso Gabas.
Haka kuma, kungiyar ta masu fafutukar ta bayyana shirinta na gudanar da ayyukanta a wannan shekarar ta 2022.Daraktan kungiyar ya ce, kungiyar za ta yi yakin neman a saki shugabanta, Nnamdi Kanu ba tare da wani sharadi ba.Edoziem ya ce, ya kamata ‘yan kungiyar tasu su shirya wata zanga-zanga a duniya, tare da maida hankali kan ofishin jakadancin Burtaniya, da ofishin jakadancin Najeriya, da ofishin jakadancin Kenya, da kuma Majalisar Dinkin Duniya.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Edoziem da mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, ta ce, “Abubuwan da ke biyowa, wasu shirye-shirye ne da ayyukan da shugabanni za su yi da gaske a wannan shekara ta 2022.“Waɗannan su ne waɗanda za mu iya bayyanawa a fili a yanzu. Za a sanar da wasu a lokacin da ya dace.”“a mu gabatar da gangami a duk faɗin duniya, don ganin an saki Onyendu Mazi Nnamdi Kanu.
A ci gaba da wannan gangamin, ana kira ga daukacin ‘yan uwa masu fafutukar kafa kasar Biafra, da abokan kasar Biafra da su canza hotonsu a shafukan sada zumunta da hoton gangamin da kujgiyaryar zata samar.“Na biyu kuma ana umurtar dukkan iyalan kungiyar ta IPOB a duk duniya,da su sabunta umarnin da aka ba su a baya.
Za mu fara zanga-zangar a manyan biranen duniya. Babban abin da za mu mayar da hankali a kai shi ne ofisoshin jakadancin Burtaniya, Majalisar Dokokin Burtaniya, Ofishin Jakadancin Kenya, Ofishin Jakadancin Najeriya da kungiyoyin kasa da kasa kamar UN, EU, Amnesty International da kuma gidajen yada labarai.”