
‘Yan adai daitan sun dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar litinin.
Matukan za su ci gaba da gudanar da ayyukansu gaba daya daga ranar Alhamis.
Lauyan kungiyar masu hawan keke, Barr. Abba Hikima Kano a yammacin Laraba.
Abcnews ta labarta cewa, mahaya babur din sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7 domin nuna rashin amincewarsu da biyan N100 na sabunta lambar rajista da kuma biyan N100 duk rana da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA ke yi.
Barr. Hikima ya ce an dauki matakin dakatar da yajin aikin ne bayan wata ganawa da shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Kano, Aminu Gadanya, da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, Baffa Babba Dan-Agundi.