Jam’iyyar PdP a jihar Kwara, ta yi kira ga tsohon shugaba majalisar Dattawa ta Nijeriya, Abubakar Bukola Saraki day a tsaya takarar shugabancin kasa a Jam’iyya, a zaben mai zuwa na shekarar 2023.
Wannan yana cikin matakin da yankin Arewa ta tsakiya ya dauka na amincewa da shi a matsayin dan takarar da ya dace.
Masu neman ganin Shugabancin kasa ya fito daga yankin Arewa ta Tsakiya a karkashin jagorancin tsohon Gwamna Mohammad Shaba Lafiagi, sun ziyarci Ilorin babban birnin jihar a karshen mako.
Lafiagi ya ce akwai yarjejeniya tsakanin jihohin Arewa ta Tsakiya cewa, Saraki ya tsaya takara. Ya kuma ce, ziyarar neman shawarwarin da aka kai a jahohin yankin Arewa ta tsakiya ya haifar da sakamako mai kyau, wajen ganin Sanata Saraki ya tsaya takara. Sanata Lafiagi ya kara da cewa, wasu ‘yan PDP sun yi alkawarin ba za su yi wa wani dan takarar shugaban kasa aiki ba sai Saraki. Har ila yau,
Shi kuwa Alhaji Abubakar Baraje cewa ya yi, “ kasancewar Sanata Saraki wanda ya riki mukami a matsayin gwamna na wa’adi biyu, da kuma shugabancin Majalisar dattawa, sun ba shi fifiko a tsakanin sauran masu bukatar tsaya wannan mukami.”