
Jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, NSCDC, sun tabbatar da cafke wasu mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka tsere daga unguwar Magami da ke Gusau jihar Zamfara, sakamakon yadda jami’an tsaron suka yi musu kofar raggo.
Majiyar ta ruwaito cewa,Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Ikor Oche, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai, inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne jiya a tashar mota da ke Gusau.
Oche ya ce an kama wadanda ake zargin ne da sanyin safiya, yayin da suke kokarin shiga wata mota da za ta nufi Taraba yayin shiga cikin sauran fasinjojin.
Ya ce, wadanda aka Kaman Tukur Halilu,dan shekara 27, ya fito ne daga kauyen Gabaru, gundumar Nahuche, a karamar hukumar Bugudu a jihar, kuma yana karkashin wani fitaccen shugaban‘yan fashi mai suna Magajin Kaura.
A cewarsa, an tabbatar da cewa Halilu na yin satar shanu a dukkan kauyukan da ke kusa da karamar hukumar.
Ya ce wasu mutum biyu da ake zargin, Hussaini Altine, dan shekara 40 da Abubakar Altine mai shekaru 60, sun fito ne daga kauyen Agama lafiya da ke unguwar Rijiya a karamar hukumar Gusau.