
Hukumar da ke kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA, ta ce za ta kaddamar da bincike kan musabbabin gobarar da ta afku a safiyar Lahadi a daya daga cikin manyan kantunan kasuwanci da ke Abuja mai suna, ‘Next Cash and Carry’ inda aka yi asarar kayayyaki da kadarori da aka kiyasta sun kai biliyoyin Naira.
Wutar ta tashi da sanyin safiya a yankin gundumar Jahi,.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello wanda ya bayyana kaduwa da alhininsa akan gobarar ya ce, gwamnati za ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Ministan a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mista Anthony Ogunleye ya fitar, ya kuma jajanta ma masu kamfanin da ma’aikatansa da kuma ‘yan kasuwar babban birnin tarayya Abuja kan lamarin.
Matakin Ma’aikatar babban birnin tarayyar ya biyo bayan kai farmaki kan kasuwar ne da masu wasoso suka kai,inda suka yi awon gaba da kayayyakin amfani na gida da dama kamar katifu da na’urorin lantarki da kayan abinci da dai sauransu.
Kayayyaki da dama ne suka kone da kudinsu ya kai biliyoyin Naira a gobarar.
An ce motar kashe gobara ta samu matsalar da ba za a iya amfani da ita ba, lamarin da ya sa manajojin kamfanin jiran agajin gaggawa.
Ministan ya yabawa hukumar kashe gobara ta babban birnin na tarayya, da ma’aikatan kashe gobara na sojojin ruwa na Najeriya da sojojin sama da kuma Guards Brigade da Julius Berger Nig. PLC, da suka agaza da kayan kashe gobara.
Hakazalika, ya yabawa hukumar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa da jami’an tsaro da sauran masu kai dauki wajen dakile gobarar.
Malam Bello ya kuma ba da tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin tashin gobarar a kokarin da ake na hana sake afkuwar haka a duk wata cibiyar kasuwanci da ke cikin babban birnin tarayya Abuja,in ji sanarwar.