
Hatsarin mota a Bauchi ya yi sanadiyar rayuka sha biyar Mutan shida sun jikkata a rana day
A wani lamari da ya zama ruwan dare gama gari a jihar Bauchi, wasu munanan hadurran motoci guda biyu sun afku a ranar Alhamis inda suka yi sanadin mutuwar mutane 15.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta ce hadurran sun afku ne da misalin karfe 12:30 na rana, kuma an ruwaito su da misalin karfe 12:35 na rana a kauyen Haka Yafi da ke kan titin Bauchi zuwa Jos.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, lamarin na farko ya hada da motoci biyu da suka taho daga wata hanya, ta biyun kuma ta faru ne bayan sa’o’i 11 a Kafin Liman da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano da misalin karfe 11:30 na dare tare da motoci uku.
A cewar kwamandan sashin, Yusuf Abdullahi, motocin biyu da suka yi hatsarin na farko motocin kasuwanci ne, karamar Bas Sharon, mai lamba YLA 88 ZY, da Toyota Hiace mai lamba KUJ 182 TU.
Ya ce, motoci uku da suka yi hatsarin na biyu, wadanda suka tare hanya, tirelar DAF ce mai lamba 1KMC95YU; Ford Sharon mini bas mai lamba NNG21MG; da Opel Vectral mai lamba BAU490AA.
Sai dai Kwamandan ya dora alhakin faruwar hatsarin na farko a kan keta gudu da direbobin biyu Mustapha Adamu da suka tuka Sharon da kuma direban motar Toyota Hiace da ba a tantance ba a yayin aikin ceto da jami’an FRSC suka yi.
Rundunar ‘yan sandan ta ce mutane tara ne dukkansu maza ne suka yi hatsarin na farko inda biyu daga cikinsu suka samu raunuka aka kaisu asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin yi musu magani yayin da aka ajiye gawarwaki bakwai a dakin ajiyar gawa na asibitin.
Rahotanni sun kuma nuna cewa mutane 12 da suka kunshi maza tara (9) da mata uku (3) ne suka yi hatsarin na biyu tare da asarar rayuka takwas (8) wadanda suka hada da biyar (5) maza da mata uku (3).
An kwashe gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kafin Madaki domin samun kulawar gaggawa da kuma tabbatar da wadanda suka mutu a hukumance.
An kuma bayyana cewa, kayayyakin da aka kwato daga wurin da hatsarin na farko ya afku sun hada da nau’ikan wayoyin hannu guda shida (6) da kuma kudi N109,090 yayin da aka kawar da duk wani cikas da aka samu wajen zirga-zirgar ababen hawa cikin sauki.