
Sakamakon dakatar da zirga-zirgar daga Nijeriya zuwa kasar Saudi Arabia da Saudiyyar ta yi a ranar laraba da ta gabata,akwai yiwuwar kamfanonin jiragen sama da fasinjoji su tafka asara, haka kuma wannan dakatarwa ta jefa fargaba da rudani ga masu yawon bude ido da kamfanonin jiragen.
Kafar yada labara ta Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane da dama sun riga sun biya kudaden ajiya na Otel da sauran bukatu, wanda zai yi wahala a mayar masu da kudaden.
Wasu daga cikin ma’aikatan a Kano da Abuja da kuma Legas sun ce sun fara lissafa asarar da suka yi ne saboda dokar hana fitar ta zato ba tsammani. Sun shaida ma majiyarmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, baya ga yin jigilar jirage da otel-otal ga dubban fasinjojin da za su je Saudiyya, sun kuma kashe makudan kudade wajen sayan biza da kuma kammala kayan aiki.
Wasu matafiya sun bayyana kaduwarsa da faruwar lamarin, inda suka ce haramcin ya kawo cikas ga tsare-tsare da kasafin kudi.
Hukumomin Saudiyya a ranar Laraba sun yi Allah wadai da dokar hana zirga-zirga da Najeriya saboda bambancin cutar corona samfurin Omicron ya bambanta da na COVID-19.
Saudiyya ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta sanya dokar hana zirga-zirga a Najeriya bayan da Ingila da Canada da a baya suka hana zirga-zirgar jiragen Najeriya sakamakon karuwar cutar Omicron.
Najeriya ta sami karin mutane uku da suka kamu da cutar Omicron a ranar Talata, wanda ya kara adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa biyar tun bayan barkewar cutar.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa (GACA) a kasar Saudiyya ta tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya a wata takardar da ta aikewa dukkanin kamfanonin jiragen sama da ke aiki a kasar ta Saudiyya.
A cikin sanarwar mai taken ‘Dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Tarayyar Najeriya da kuma zuwa Tarayyar Najeriya’, GACA ta ce, “Dakatar da dukkan jiragen da ke shigowa da kuma dakatar da shigowa cikin Masarautar ga wadanda ba ‘yan kasar ba da ke zuwa kai tsaye ko a fakaice daga Tarayyar Najeriya. sai dai hanin bai shafi wadanda suka shafe kwanaki 14 a wata kasar da aka ba su izinin fitowa.