Daga: Abdulmalik Saidu Maibiredi
SSA NEW MEDIA
Gwamnatin jihar Zamfara a karkashin jagorancin Hon Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun, ta jagoranci ceto ma’aikata 183 da iyalansu da ke zaune a unguwar Daza, da ke Garin Gusau, daga karbe gidajensu da bankin mortgage ya shirya yi.
Zaman ya gudana karkashin jagorancin gwamnan wanda Shugaban ma’aikata, Alh. Kabir Muhammad Gayari ya ke wakilta; ya jagoranta inda ya ji bangarorin biyu, na bankin Mortgage da kuma na mazauna wannan unguwar.
Da aka zo domin karbe gidansu ganin shekaru sama da bakwai da gina masu su, amma har yanzu ba Wanda ya fara biyan ko naira.
Da ya ke jawabi wajen zaman, Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, tun farko an tafka kuskure wajen hanyar da aka bi don bayar da gidan. Wanda shi ne ya haifar da halin da ake ciki yanzu.
Daga nan ya bayar da tabbacin cewa, zamowar gwamnati uwar kowa, da kuma irin jinkan Gwamna Matawalle, ba za ta bari wani ma’aikacinta ya fita cikin wannan gidan ba.
Kuma gwamnatin za ta shiga ciki dumu-dumu domin tabbatar da an sharewa ma’aikatanta hawaye.
Da su ke jawabi wajen zaman, al’ummar unguwar sun nuna matukar godiya ga gwamantin Matawalle, musamman na Samar masu da abubuwan more rayuwa a unguwar, musamman tituna, uwa uba wannan yunkuri na tabbatar da gidajensu sun zama mallakarsu.
Zaman shiga tsakanin wanda ya gudana a harabar gidajen, ya samu halartar Manajan bankin reshen jihar Zamfara Haj. Hadiza Modibo da ma’aikatanta, Shuwagabannin Kungiyar Kwadago na jihar Zamfara da Kungiyar mazauna unguwar.